Jack Wilshere yasamu shiga cikin tawagar yan wasan Arsenal da zasuje atisaye a kasar Dubai.
Jack Wilshere wadda yake atisaye da Arsenal a yanzu haka zaibi tawagar yan wasan Arsenal zuwa kasar Dubai dan yin Atisaye.
Sai dae haryanxu babu tabbas akan ko Arsenal zasu bawa Wilshere kontaragi ko da na watanni shida ne.
Dan wasan gaban Arsenal Pieer Emrick Aubameryang haryanzu baidawo atisaye acikin tawagar yan wasan Arsenal ba.
Aubameryang wadda yasami damuwa da kungiyar Arsenal sakamakon karya dokar kungiyar da yayi nakin zuwa atisaye da wuri.
Babu tabbas koh Aubameryang zaibi tawagar yan wasan Arsenal zuwa atisayen da zasuje a kasar Dubai.
Haryanzu dae dan wasan yana atisaye ne shi kadae batare da Tawagar yan wasan Arsenal ba. Hakan yasa ake tunanin ko dan wasan zai bar kungiyar Arsenal a wannan lokacin.
Kungiyar El Nassr ta kasar Saudi Arabia sun kawowa Arsenal tayin neman aron dan wasan da yarjejeniyar siyansa daga baya. Inda haryanzu Arsenal basu ce komai akan wannan tayi na El Nassr ba.
Sai dae wasu rahotanni na nuna cewa Aubameryang yayi watsi da wannan tayin sabida bai shirya koma taka leda a yankin larabawa a wannan lokacin ba. Rahoton yace Aubameryang yanaso yaci gaba da taka leda ne a nahiyar turai, dan haka zai amshi tayi ne kawai idan yazo masa daga nahiyar turai.