HALIN DA AKE CIKI AKAN VLAHOVIC!!
Arsenal Suna cikin rudani wurin ganin sunsami dan wasan gaba da zai taimaka masu su kare a gasar Primier League acikin Top 4th.
A yanzu haka Arsenal suna duba yiwuwar karban tayin kungiyar El Nassr da takawo wurin neman abasu aron Aubameryang da yarjejeniyar siyansa £8m a karshen wannan kakar wasan.
Tun bayan fitan Aubameryang Arteta ya cire daga cikin tawagar yan wasan Arsenal, Arteta Yana amfani da Lacazatte da kuma Nkethia a matsayin yan wasan gaba masu zura masa kwallo a raga. Sai dae Yan wasan biyu sun'nuna bazasu iya ba sakamakon kwallo uku kadai suka iya zurawa a raga a wannan kakar wasan.
Hakan yasa Arsenal suke neman dan wasan gaban da zai taimaka masu wurin samun mataki na 4th a gasar Primier League.
Dusan Vlahovic shine dan Wasan gaban da Arsenal ke nema dan maye gurbin Aubameryang sai dae Arsenal sun fuskantar kalubale matuka wurin ganin sun dauke dan Wasan.
Wakilin (Agent) dan wasan dashi kansa dan wasan (Vlahovic) basu da bukatar barin kungiyar Fiorentina a wannan lokacin. Wakilin dan wasan yana son sai ankare wannan kakar wasan sannan dan wasan yanemi barin kungiyar dan yasan a wannan lokacin kungiyoyi da yawa zasu shigo neman dan wasan, wadda hakan zai basu damar zabar kungiyar da take zuwa gasar Champion league a kowana Shekara.
Hakan yazama abu mai matukar wahalar gaske wurin shawo kan dan wasan domin ya amince yabar Fiorentina a wannan lokacin.
Wannan dalilin yasa Arsenal acikin wani hali, inda haryanzu suke duba yiwuwar ko su amince da tayin kungiyar El Nassr akan Aubameryang? Ko kuma sudawo da Aubameryang cikin tawagar yan wasan, sujira zuwa karshen wannan kakar wasan wurin neman wani dan wasan gaba?
Wannan shine halin da ake ciki a Yanzu.
Komae zai iya faruwa, Arsenal suna iya juya ra'ayin Vlahovic da kudi, amma zuwa yanzu abune mai wahalar gaske Vlahovic ya amince ya bar Fiorentina a Yanzu.
Wannan shine labarin da nagani wadda Charles watts ya wallafa a shafinsa a dazu.