Arsenal na sha'awar siyan golan Amurka Matt Turner wanda hakan zai sa Bernd Leno ya bar kungiyar.
Leno ya sauka daga kan mukaminsa a Arsenal, Inda Aaron Ramsdale ya Maye Gurbin da a matsayin sabon No1 tun lokacin da ya koma kungiyar a bazara.
Tun da farko an yi tunanin Leno zai tafi a karshen kakar wasa, amma zuwan Turner zai iya canza hakan.
Arsenal na zawarcin dan wasan mai shekaru 27, wanda ke taka leda a kungiyar New England Revolution ta MLS da kuma tawagar kasar Amurka.
Turner ya kasance cikin kyakkyawan yanayi a kwanan nan, inda ya lashe Gwarzon mai tsaron ragar MLS a kakar da ta wuce kuma ya fito a wasan All-Star shima.
A yanzu dai Arsenal na neman mai tsaron ragar, inda rahotanni daga Amurka ke cewa za'a kashe kusan fam miliyan 5.5 wajen siyan mai tsaron ragar.
Shi kuwa Leno ana alakanta shi da kungiyoyi da dama da suka hada da Newcastle da Inter Milan. Ana tunanin bangarori a Jamus suna zawarcinsa.