DAN WASAN TSAKIYAR DA ARSENAL TAKE NEMA YA FADI MAGANA MARA DADI


Dan wasan tsakiyar da arsenal take nema Dan m  Wolves:yace kungiyar Arsenal sunyi murna kamar sun lashe gasar Premier League bayan kammala wasan su. Na ranar alhamis a gidan Wolverhampton
 

Dan wasan na tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Wolves Ruben Neves yace Arsenal sunyi murna tamkar sun lashe gasar Premier League lokacin da suka doke Wolves a ranar Alhamis.a Gida bayan korar Daya Daga cikin yan Wasan arsenal martinelli

Kungiyar ta Arsenal ta koma mataki na biyar agasar Premier League bayan nasarar da ta samu akan Wolves daci 1-0 

Dan wasan Ruben Neves yace: “Munyi duk abunda yakamata amma bamu samu nasara ba ansamu nasara akan mu

“Hakan zai bamu damar kara dagewa da kuma duba wasu kuskuren mu domin mu gyara a wasa na gaba, Dama ita faduwa gyara ce. Amma kwallon da suka jefa mana akwai keta ko babu wannan itace kwallon kafa. Bamu da damar cewa komai akan hukuncin da alkalin wasa ya yanke

“Muna bukatar mukara dagewa wajan  habbaka jefa kwallo a raga, Saboda muna kirkirar damar maki amma bama samun sakamako me kyau ba,
“Na karbi hukuncin da aka yanke akan kwallon da aka zura mana, Amma irin kwallon nan a wani wasan ana bada ita a wani wasan kuma ba a bayarwa. ba, Yakamata ace su zama masu yanke hukunci iri daya saboda irin wannan abun takaici ne agare mu.

“Munga ta hanyar yadda Arsenal suka bi wajen murna bayan sun samu nasara a wasan. Bantaba ganin Arsenal suna murna irin wannan ba sama da shekaru 10 da suka gabata – Abun akwai mamaki kace sun lashe gasar Premier League.” ta wannan Shekarar

Magana ta gaskiya wannan dan wasan yana da son zuciya wajan yin magana akan arsenal yanzu Wannan murnar harta fi nasarar cin F.A Cup?

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post