Mikel Arteta ya tabbatar da cewa Arsenal za ta fara tattaunawa da Bukayo Saka.
“Tabbas burinmu shi ne mu ci gaba da rike Bukayo har tsawon lokacin da zai yiwu saboda muna matukar farin ciki. Yanayin da yake ciki daga cikin kulob dinmu"
Arteta: "Tattaunawa ce da za mu yi da ɗan wasan, sannan wakilinsa, danginsa - waɗanda za su kasance masu mahimmanci kuma - don haka kowa yana cikin maganar
"Muhimmancinsa a cikin ƙungiyar ba abin tambaya bane kuma muna son ci gaba da hazakarmu, tabbas hakan ne."
Mikel Arteta akan bukatar Arsenal don karfafa kungiyar a bazara:
"Tabbas za mu sayi 'yan wasa a lokacin bazara, ba tare da wata shakka ba."
Wasu rahotanni Daga Belgium: since Arsenal na matukar sha'awar siyan Youri Tielemans kuma dan wasan yana shirin barin Leicester. City inda kungiyar tana son karbar tayin fan miliyan 35.
" Arteta ('yan wasa masu inganci za su koma Arsenal)
“Kwarai kuwa. Muna da al'ada, abin da kulob din ya zabarwa kansa abin da muke a matsayin kulob, yana da girma. Kowa"
Arsenal ta yi watsi da tayin da aka gabatar mata kan ɗan wasan Masar a watan Janairu Mohamed Elneny daga Newcastle, Leeds da Watford, duk da cewa kwantiragin matashin mai shekara 29 na gab da karewa a watan Yuli. Ko Mai Hakan yake Nufi arsenal zata kara Mai kwantaragi ne?