ABUBUWAN DA YA KAMATA KUSANI AKAN KARAWA TSAKANIN ARSENAL DA SEVILLA

"CUP EMIRATES" 🏆

Arsenal vs Sevilla
Asabar 30 ga Yuli @ 12:30 UK TIME
Match Preview

A ranar Asabar da yamma ne za a dawo gasar cin kofin Emirates karo na 11, yayin da Arsenal za ta karbi bakuncin Sevilla a Arewacin London a wasan sada zumunta na karshe.

Gunners ta dauki kofin a gasar cin kofin Emirates sau biyar daga cikin 10 da da aka buga  yayin da Los Palanganas ta zama ta biyu a 2017.

Brentford ta samu nasara a kan Mikel Arteta da ci 2-1 a filin atisayen Gunners na London Colney cin da ya dan kawo rudani bayan wani lokaci mai ban mamaki.da kungiyar tayi a wasannin share fage .

Da sabbin ‘yan wasa Gabriel Jesus da Oleksandr Zinchenko tuni suka yi tasirin da ake so, acikin tawagar  Arsenal inda  ta doke Ipswich Town da Everton da Nuremberg da kuma Orlando City kafin daga bisani ta  sake jefa kwallaye hudu a ragar Chelsea a wasan share fage a farkon wannan watan.

Arteta ya so ya jaddada nasarar  ta doke Blues da ci 4-0 "cewa irin wannan nasarar ba ta ba da garantin " amma kyakkyawan fata ya kasance mafi girma da ya dade a cikin zuciyar magoya bayan Gooners, koda kuwa kungiyar tayi rashin nasarar akan Brentford  hakan bazai zama wata matsala ba,

Gunners na da damar ta karshe don kawo karshen wasanninta na tunkarar kakar bana kafin fara sabon kakar wasannin Premier da Crystal Palace a ranar 5 ga Agusta, amma gasar cin kofin Emirates na baya-bayan nan a 2019 Arsenal ta  sha kashi da ci 2-1. agun Lyon.

gasar cin kofin Emirates  wasanni hudu, Arsenal ta samu nasarar daukar kofin a shekarun 2007, 2009, 2010, 2015 da 2017, amma Sevilla zata Kasance ba bakuwa  ce wajen fuskantar hamayya ga kungiyar ta Arewacin London.

Julen Lopetegui ba zai tafi da tawagarsa ta Sevilla zuwa Ingila don ganin abubuwan da suka faru ba, saboda dole ne Los Palanganas ta yi tattaki don karawa da Leicester City sa'o'i 24 bayan an kammala wasansu na cin kofin Emirates da Gunners.

A daidai lokacin da suka fara wasan share fage da abokan hamayyar Arsenal Tottenham Hotspur a Koriya ta Kudu, Sevilla sun yi kunnen doki 1-1 da Lilywhites kafin su samu nasara a kan Sporting CP a Trofeu Cinco Violinos a bugun fanareti, 

Lopetegui dai ya buga wasanni uku na tunkarar kakar wasa ta bana ba tare da shan kashi a hannun  wata kungiyar ba sun ci Angers  6-0 a ranar Laraba, inda Lucas Ocampos da Erik Lamela da Youssef En-Nesyri suka zura kwallo a raga, 



Tsarin shirye-shiryen Arsenal:

wasu daga cikin masu jinya na yau da kullun na Arsenal a wannan bazarar, sune Kieran Tierney da Takehiro Tomiyasu duka biyu sune  cikin shakku a fara buga gasar Premier  da su ba,  bai kamata a yi kasada saka su a wasa ranar Asabar ba.

Emile Smith Rowe kuma yana jinyar ciwon tsoka, yayin da sabon sa hannu Fabio Vieira har yanzu bai fara buga wa kungiyar wasa ba saboda matsalar idon sawu, kuma da wuya shi ma ya murmure kafin gasar cin kofin Emirates.din

Sai damuwar raunin da Gabriel Jesus ya samu bayan an dauke shi da wuri a karawar da suka yi da Chelsea, amma Eddie Nketiah - wanda ya zura kwallo daya tilo a Wasan da Arsenal tayi a karawar da Brentford a ranar Laraba - a shirye yake a fara da shi, daga baya Jesus ya shigo ciki

Arsenal zata iya farawa: 

Ramsdale; White, Saliba, Gabriel, Zinchenko; Xhaka, Partey; Saka, Odegaard, Martinelli; Nketiah

Sevilla kuma zata iya farawa da Wannan jerin

Bono; Navas, Gudelj, Rekik, Acuna; Jordan, Delaney; Corona, Gomez, Ocampos; En-Nesyri

Mun ce: Arsenal 2-1 Sevilla

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post