Sanarwa a HuKumance: daga
www.arsenal.com >>>
Nuno Tavares ya koma Olympique Marseille ta Ligue 1 a matsayin aro na tsawon kaka.
Dan wasan baya na hagu, mai shekara 22, ya hade da kungiyar Kwallo kafa ta Arsenal a lokacin bazarar 2021 daga Benfica, kuma ya buga wasanni 28 a duk wasannin da ya buga a kakar da ta gabata, inda ya zura kwallo daya kuma ya taimaka sau biyu.
Dan wasan na Portugal na kasa da kasa da shekara 21 ya zira kwallo a wasansa na farko a kungiyar, inda ya zura kwallo a raga a wasan sada zumuncin da muka yi da Rangers a watan Yulin 2021.
Kwallon farko da Nuno ya zura a Arsenal a gasar Premier itace Lokacin da muka ci Manchester United a gida da ci 3-1 a watan Afrilu.
Kowa a Arsenal yana yiwa Nuno fatan alheri a kakar wasa mai zuwa tare da Marseille.