EDU GASPAR YA FADI DALILIN DA YASA ARTETA YA ZAMA KOCIN ARSENAL!!

EDU GASPAR AKAN DALILIN DA YASA YAZABI ARTETA A MATSAYIN KOCIN ARSENAL!!


Lokacin da na hadu dashi, naje har gidansa, muna da kyakkyawar alaka da juna kai tsaye muka fara tattaunawa.

Naga mutumin da yake da tsari a harkan kwallon kafa, salon wasan da yakeso ya buga, da kuma irin yan wasan da yakeso yayi amfani dasu. Wadda wannan shine abinda mukeso.

Yanayin yadda yakeso yayi wasa da kuma irin mutanen da yakeso yayi aiki dasu aciki da wajen Arsenal. Abuuwan dai suna da yawa. Amma ya bayyana min yana da tsarin yadda yakeso yayi wasan ƙwallon ƙafa.

Wadda wannan tsari nasa yana bamu sauki sosae wurin zaban dan kwallon da zamu siya.
[
Edu a kan kasancewar sa  silar da Arsenal ta siyo Gabriel Jesus: 

A'a, ba ni bane. Arsenal ce da kanta tayi wannan aiki.  Ni dai kawai ina cikin wani  bangare ne na tat'taunawa da yan wasa lokacin da za'a siye su.

 A matsayinmu na kungiya  dole ne mu yi alfahari da samun dan wasa kamar Gabriel Jesus.

Source  [Sky Sports]

✍️✍️✍️
Prince Tije

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post