Gabriel Martinelli ya yi cikakken bayanin yadda ya shawo kan abokin wasan sa na Brazil Gabriel Jesus ya koma Arsenal a bazara.
Gunners sun amince da yarjejeniyar fan miliyan 45 da Manchester City domin sayen Jesus, wanda ya kasance daya daga cikin manyan ‘yan wasan kungiyar.
Dan wasan mai shekaru 25 ya yi aiki tare da kocin Arsenal Mikel Arteta a filin wasa na Etihad, inda ya taimakawa City ta lashe kofunan Premier hudu.
Jesus ya ya Fahimci Arsenal cikin sauri inda ya zira wasu kwallaye a raga a farkon kakar wasa kuma ya riga ya nuna halayensa da yawa a kan abinda zai iya da kwallon.
Har ila yau Arsenal ta dauko dan wasan Brazil Marquinhos daga Sao Paulo, inda ya hade da takwarorinsa Martinelli da Gabriel Magalhaes a cikin tawagar farko.
Da yake magana da gidan tv na tare da Ian Wright akan faifan gidan Wrighty's House, Martinelli yayi cikakken bayanin yadda shi da mai tsaron baya Gabriel suka ci gaba da rokon Jesus da ya hada kai da su a filin wasa na Emirates.
"A cikin tawagar kasar, na kasance [yana cewa] kowace rana, "Gabi, kai abokin wasa ne, ka zo mana, muna bukatar ka (a Arsenal),"
‘Gab [Gabriel] kuma, babban Gabi [yana roÆ™on Jesus ya shigo Mana