Mikel Arteta: Akan raunin Tomiyasu.
Ya kusan fara yin wasu atisaye ina fatan mako mai zuwa.
Fabio [Vieira]
mai yiwuwa ya ɗan daɗe, ina tsammanin yana buƙatar wani mako ko makamancin haka kafin ya fara atisaye da abokan wasansa. Ya yi rashin sa'a da yazo Arsenal ta wannan hanya.
Akan Gabriel Jesus.
Ya sami bugawa a cinyarsa tun a zangon farko na wasan. Yaji bazai iya ci gaba da buga wasan a haka ba, wannan dalilin yasa muka chanza shi sabida bamu son muyi wata kasada akansa.
Arteta: Akan Saliba:
Na yi matukar farin cikin ganin yadda yake taka leda, yadda ya saba da kungiyar, da yadda yake nuna gogewa duk da kasancewar yana dan shekaru 21 ne kawai. Ina fatan ya ci gaba da hakan. Za mu ci gaba da ginashi, sabida yana da damar zama babban dan wasa, a yanzu haka ya riga ya zama babban dan wasa kuma dole ne mu kara gogar dashi.
✍️✍️✍️
Prince Tije