WATA SABUWAR MAGANAR AKAN WILLIAM SALIBA

Tuni dai William Saliba ya amince ya rattaba hannu akan sabon kwantaragi a Arsenal, in ji dan jarida Freddie Paxton.

Har yanzu mai tsaron bayan Faransa bai buga wasa a hukumance a kungiyar ta Gunners ba tun bayan da ya kammala komawarshi akan fam miliyan 30 a bazarar 2019.

Maimakon haka, ya yi zaman aro uku a gasar Ligue 1, na baya-bayan nan shi ne tare da Jorge Sampaoli na Marseille - inda ya haskaka har  aka ba shi kyautar gwarzon matashin dan wasan Ligue 1 na shekara.

Yanzu, guru Paxton ya shiga shafin Twitter yana cewa: "A fahimtata ne William Saliba ya riga ya amince da sabuwar yarjejeniya don tsawaita kwantiraginsa [Arsenal] bayan tattaunawa mai kyau kafin Zuwa Amurka.

Arsenal ta gamsu da ci gabansa kuma tana ganin shi a matsayin wani muhimmin bangare na cigaba kungiyar anan gaba"

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post