WATA TATTAUNAWA EDU DA JARIDAR KAYA KAYNAK DAKE LONDON.AKAN WANI..

 Tattaunawar Edu Da Jaridar  Kaya Kaynak dake London.

 Edu Gaspar: Tare da dukkan girmamawa, shirin ya fara da gaske lokacin da muka yanke shawarar korar  Unai Emery, Inji Edu. Wannan shi ne shirina na farko – naje wurin hukumomin kungiyar Arsenal na  bayyana musu dalilin da ya sa muke bukatar chanza mai horaswa, dalilin da ya sa muke son komawa wata hanya ta daban.

 Manufar da ke tattare da hakan itace  samun koci mai cikakken ra'ayi. Wadda yake da tsari mai haske. Wadda yake da  tsarin  yadda yake son yin wasa. Kuma daga haka za mu gina wani abu tare.

 Dole ne mu kasance da ƙarfin hali don yanke shawara a tsakiyar kakar wasa. Hukumomin Arsenal sun ce da ni wow, ba mu taba yin haka ba. Ko da yake mun yi hakan amma da dadewa.  Nace hakan ba matsala bace, amma  idan kun riga kuna ganin hakan  ba shirinmu bane, sai a chanza.

 Idan  ba haka ba za kuyi ta  jinkirta, jinkirta, jinkirta yin abubuwa a wasan kwallon kafa.

A  wasan ƙwallon ƙafa wani  lokaci yana da kyau ku dinga yanke  shawara cikin sauri. Yin hakan yana dab zafi,  da kuma  kalubale., amma dole ne a yi.

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post