GRANIT XHAKA YA BAYYANA HALIN DA YA SHIGA LOKACIN DA ARTETA YA ZAMA KOCIN ARSENAL

Granit Xhaka:

“Lokacin da aka nada Mikel, na gaya masa cewa ni bazan zauna ba ina so in tafi.

Ya kuma fahimceni gaba daya.

Mun yi hira ta biyu bayan 'yan kwanaki kuma nanma nafada masa zan tashi lokacin da na shiga, na yi magana da matata.

"daga baya Sai Mikel ya fara min magana akan  yadda na kasance babban bangare na shirye-shiryensa. Ina sonsa domin  Ya kasance mai gaskiya, 

a raina Na ji zan iya amincewa da shi. Ya ce min in ba shi wata shida don ya tabbatar min da cewa ina cikin tsarinsa , sannan in har yanzu ina son tafiya, ba matsala.sai in tafi”

“Yawanci ina kashe lokaci mai yawa wajen yanke waɗannan shawarwari. Ina magana da duk wanda ke kusa da ni, amma a ranar na karya dokokina.

Na ce wa Mikel, 'Ok'. Na kira matata da iyayena, 'nace musu zamu zauna sannan na  Buɗe jakunkuna na wannan sabon ƙalubale ne.

Ko dai kuna tare dani kokuma inkasance  ni kadai kaɗai."

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post