Tsohon dan Wasan Arsenal da Chalsea Olivier Giroud a tattaunawa da Sky Sports: "Ina kallon Arsenal har yanzu. Ina tsammanin wannan za ta zama wata shekara mai ban sha'awa a gare su."
Lokacin da aka matsa masa musamman ko ya yi imanin cewa Arsenal za ta yi nasara a matsayin kungiyoyin hudun farko a teburi a bana, Giroud ya kara da cewa: "Eh, tabbas, ina fata."
Arsenal na da kwarin gwiwar cewa za su iya samun sabon ranar da za su buga wasansu da PSV nan bada dadewa ba badan komaiba saidon gudun bata tsarinsu akan wasan. UEFA na aiki tare da kungiyoyin biyu don nemo mafita da tattaunawa kan sabuwan ranar.
Ana sa ran Thomas Partey zai kasance cikin tawagar da za ta kara da Brentford a karshen mako, yana atisaye tun makon da ya gabata.
[Charles Watts.]