Arsenal tana sha'awar kashe fan miliyan 30 don siyan dan wasan Shakhtar Donetsk Mykhaylo Mudryk.
Fara kakar wasa da Arsenal ta fara yi a kakar wasa ta bana ya karfafa aikin kungiyar a kasuwar musayar 'yan wasa kuma Gunners din sun nuna suna sha'awar 'yan wasan da suke ganin na musanman ne
Gunners ta lashe wasanni biyar na farko a kakar wasa ta bana, kuma tana kan teburin gasar Premier, duk da rashin nasarar da suka yi a hannun Manchester United da ci 3-1 a karshen makon da ya gabata.
Mikel Arteta ya kawo kwararrun yan wass a kasuwar musayar 'yan wasa inda ya kawo irin su Gabriel Jesus da Oleksandr Zinchenko, wadanda suka kara samar da sabon salo acikin tawagar Arsenal. Inda kungiyar tayi kokarin ganin ta buga gasar zakarun turai Amma kungiyar Tottenham ta sha gaban kungiyar ta Arsenal
Amma Wannan shekarar Mai Horarwa yayi Babban shiri akan Hakan Dan Kasar Spain din yana cikin shekara shi ta uku Arsenal
wani rahoto yace kungiyar Arsenal tana son dan wasan Donetsk Mudryk, wanda ya ja hankalin kasashen Turai a cikin watanni shida da suka gabata.
Dan kasar Ukraine ya amince a makon da ya gabata cewa zai yi tsalle da damar shiga Gunners.
‘ Ina tsammanin kowane saurayi yana mafarki game da gasar Premier,' in ji Mudryk.
Da aka tambaye shi musamman game da Arsenal ya ce: ‘Eh, eh. Yana da wuya a ce A'a amma Arsenal kungiya ce mai kyau. Kyakkyawan koci, ina son yadda suke taka leda.'