Cinikayar yan wasa ta hunturu 🤝
Dan wasan Brézil mai taka leda a tsakiyar fili a kungiyar Aston Villa da Brazil
Douglas luiz
ya shedawa abokan Wasan shi na Aston Villa cewa Yana son komawa Arsenal a cinikayar yan wasa ta hunturu wato a janairu Kenan.
Haka itama kungiar da dayan dan Kasar Brazil din da yake taka leda a palmires Danilo tace à shirye take ta karbi tayin Arsenal a Watan na janairu
Itadai Arsenal ta garzaya neman Daya daga cikin Yan Wasan biyu bayan da Yan Wasan da Arsenal ta dorawa rai Wannan gurbin wato
Tsakiyar fili bangaren tare Thomas Partey da Mo Elneyni Suka samu rauni gabadayan su
Nan Take Dai kungiar Danilo tayi watsi da tayin Arsenal Na kimanin €m 20 da Cewa bazasu saki dan wasan ba daidai tsakiyar wasanin Kasar ta Brézil
A yayinda itama Aston Villa tayi watsi da tayin Arsenal Har sau uku a jere Na kimanin €m 25 Duk da Cewa Aston Villa ta kwana da sanin Cewa Shekara 1 ta rage a kontragin Douglas luiz
Ana tsamanin Arsenal zata koma neman Daya daga cikin su a janairu mai zuwa Duk da Cewa Yan Wasan Na Arsenal raunin nasu ba yanda Aka zata bane Zasu dawo da wuri
Wanne yakamata Arsenal ta dauka daga cikin su ?
Admin MrK ✌️