Rahotanni sun bayyana cewa Arsenal na shirin yiwa William Saliba karin albashi yayin da daraktan kungiyar Edu ke kokarin ganin ya zaunar da shi a filin wasa na Emirates na tsawan Lokaci da kuma dakile sha’awar kungiyoyin da zasu iya Neman dan wasan zuwa kungiyoyin su,
Arsenal ta shirya tsaf don sayen dan wasan gaban Juventus dan kasar Serbiya Dusan Vlahovic, dan shekara 22, da kuma dan Italiya Fabio Miretti, mai shekara 19, a kan fam miliyan 101. Source ( Sun)
Haka kuma Arsenal ta tuntubi Eintracht Frankfurt a kan dan wasan gefe na kasar Denmark Jasper Lindstorm dan shekara 22 Source:(Mail)
Arsenal da Chelsea da Liverpool da Manchester City sun sa ido kan dan wasan Sifaniya dan wasan tsakiyar Villareal Alex Baena mai shekara 21 wanda za a cefanar shi a kan yuro miliyan 35 ( Sport in Spanish)
Arsenal ce kulob mafi kyau a Ingila. A Man City da Chelsea, ba za su taba samun irin wannan salon ba." ~