WASU ABUBUWA DA SUKE FARUWA ARSENAL KUNGIYAR TA KARA KIRAWO WANI DAGA CIKIN YAN WASAN TA

TAKEHIRO TOMIYASU..

Tomiyasu ya fice daga cikin kungiyar kwallo kafa ta kasar Japan inda  ta sanar da cewa Tomiyasu ya fita daga cikin sansanin kungiyar inda wani rahoto yake cewa kungiyar Arsenal ta bukaci dan wasan ya dawo  London,

 Arsenal ta tuntubi Eintracht Frankfurt game da dan wasan gefe Jesper Lindstrom mai shekaru 22.  (Mail)

Arsenal na shirin zawarcin dan wasan Juventus akan Yuro miliyan 110
Arsenal na neman kai wa Juventus hari nan gaba kadan, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Calciomercato na tafiya tare da da'awar cewa Arsenal na shirin zawarcin Yuro miliyan 110 ga 'yan wasan Juventus Dusan Vlahovic da Fabio Miretti.

Ganin ana danganta Arsenal da Vlahovic da Miretti bai kamata ya zo da mamaki ba. Tun lokacin da Mikel Arteta ya karbi ragamar horar da 'yan wasa, Arsenal a fili yake yana son  yin aiki  da  matasan 'yan wasa masu tasowa a cikin waɗanda zai dunga daukar  dan gina kungiyar na dogon Lokaci,

 Inda yanzu yayi Imani da  wasu ƙananan 'yan wasan da ke cikin ƙungiyar ta yanzu.

Sai dai ba a ambaci lokacin da Arsenal za ta iya zawarcin ‘yan wasan ba, domin sayen manyan ‘yan wasa acikin watan Janairu abu ne mai wahala, domin  gaba daya kungiyoyi ba sa son rabuwa da manyan taurarin su  a tsakiyar kakar  wasa koma dai Maye ne, Lokaci shine zai Tabbatar da abunda zai faru

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post