MIKEL ARTETA YAYI KAK'KAUSAR MAGANA AKAN WASAN MAN UNITED

Kocin Arsenal Mikel Arteta yace yana da kwarin guiwa tawagar yan wasansa zasu iya doke Manchester United.

A yau Lahadi kungiyar Arsenal zasu kece raini da Manchester United a filin wasa na Old Trafford.

A wata hira da akayi da Mikel Arteta a yau anyi masa tambaya shin ko yana ganin tawagar yan wasan nasa zasu iya yin nasara a filin wasa na Old Trafford? Kasancewar Arsenal basu iya doke Manchester United a wannan filin wasan. 


Arteta yace bazanso wani daga cikin yan wasana yaji haka a ransa cewa bazamu iya yin nasara a filin wasa na Old Trafford ba. Sabida suna da gogewar da zasu iya zuwa wannan filin wasan kuma suyi nasara. Ina tunanin munyi imanin hakan zai faru. Idan har bamujin hakan a ranmu to zaifi kyau kawai mu zauna a gida batare da munje mun buga wasan ba.

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post