GABRIEL MARTINELLI YA BAYYANA ABINDA SUKE YAWAN CEWA AKAN JESUS

Matashin dan wasan gaban Arsenal dan kasar Brazil wato Gabriel Martinelli ya yabawa abokin wasansa wato Gabriel Jesus.

Martinelli yace Gabriel Jesus Dan Wasan wasa ne da yake da ban mamaki acikin fili da wajjen fili. Dan wasan ne da yake da natsuwa kuma kowa yana mamaki acikin tawagar yan wasan mu. Har manyan yan wasanmu wadanda suka girmewa Gabriel Jesus suna magana akansa, suna kallonsa a matsayin wani jigo a ƙungiyar.

Gabriiel Jesus yazo Arsenal ne daga Manchester City a wannan kakar wasan akan kuɗi £45m. Zuwansa yasa yan wasan Arsenal sunsamu kwarin guiwa sosae. Domin ya kasance dan wasan ne da yake aiki tukuru.

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post