Dan wasan tsakiyar Arsenal dan kasar Switzerland wato Granit Zhaka ya maida martani akan masu cewa suna murna yana yawa idan sunci kwallo.
Dan wasan wadda yake haskakawa tun bayan dawowa daga wannan kakar wasan ya ci kwallo daya inda ya taimaka akaci biyu.
Zhaka yace idan kaci kwallo bakayi murna ba, zasu dinga tambayar meyasa bakayi murna ba? Idan kayi murna zasuce meyasa kake murna? Wasu lokutan bazaka taba burge mutane ba.
Wannan shine aikinmu, shine abinda mukeso muyi, muyi farin ciki a duk lokacin da mukayi nasara, babu ruwanmu da wata kungiya muka doke.
Anyiwa Zhaka wannan tambayar ne sabida ganin irin murnar da kungiyar tayi bayan tayi nasara akan Fulham a makon da ta gabata.