Dan wasan bayan Arsenal dan kasar Scotland Kieran Tierney ya bayyana dan wasan da yafi kowa kokari a filin atisaye a Arsenal.
Tierney yace dan wasan da yafi kowa kokari a filin atisaye shine Smith Rowe, magoya bayan zasu dinga ganin kwarewarsa, amma a filin atisaye a kowana rana yana kara bamu mamaki sabida yadda yake nuna kwarewarsa.
Yana daukar kwallo acikin mutane yayi gudu da ita yayi yanka, yaci kwallo sannan ya taimaka aci. Ina matukar jindadin yin wasa a tare dashi.