Gabriel Jesus Akan Wasan Arsenal DA Manchester United



Gabriel Jesus akan wasan Arsenal da Manchester United jiya!!


A duk lokacin da aka fara zurama kwallo a wasa, wasan Yana zamowa mai wahala. To amma daga baya munzo munyi nasara a wasan wadda hakan shine abu mafi muhimmanci. Hakan ya nuna kungiyarmu sunyi kokari sosai.

Dukkan kungiyoyin biyu sun chanchanci suyi nasara. Sai dai mune mukafi dacewa da yin nasarar domin Yan wasanmu sunyi kokari sosai.

Wasa ne tsakanin kungiyoyi biyu masu hamayya da juna, wasa ne Mai wahalar gaske, wasan ya kasance tamkar gasar Primier League, domin suna da yan wasa masu basira Dole wasa dasu yayi wahala. Amma a karshe dae munyi nasara  wadda wannan shine abu mafi muhimmanci.

A takaice dae muna shirye shiryen tun karar kakar wasa Mai xuwa, dan haka kowa yayi farin ciki da wannan wasan acikinmu.

Gabriel Jesus yaci gaba da cewa... A shekarar da ta gaba wurin shiryen tun karar kakar Wasa da ta gabata nayi fama da rauni a guiwar kafata , wadda hakan ya janyo anyimim aiki a kafata dalilin hakan yasa ban buga wasanni share fagen waccan lokacin ba.  Nayi kokari wurin tursasa kaina dan ganin na buga wasannin amma a karshe hakan baisamu ba, dole akayimin aiki.

Wannan abin yabani wahala dan kadan wurin dawowata daga jinyar. Amma a wannan kakar wasan abin bahaka bane. I wannan shekarar naji dadin hutun da nayi sannan nayi atisaye sosai sannan na maida hankali akan dawowa Arsenal dan na tunkari wasanni share fage. 

Yanxu Haka inajina lafiya lau kuma a shirye nake da na buga kwallon Kafa.

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post