ARTETA YA BAYYANA DALILIN DA YASA YASIYO CALAFIORI

Mikel Arteta akan Ricardo Calafiori:

Eh tabbas nayi farin ciki. Domin mun dauki lokaci mai tsayi munasa ido akan wasansa domin munkai shekara daya. Mun sami karancin yan wasan baya a kakar wasa da ta gabata.

Mun fahimci cewa zai zama Babban dan wasa, Mai basira, wadda yake da gogewa da zai iya taimka Mana. Haka zalika dan wasane da zai iya zama Babban dan wasa a duniya nan gaba.

An tambayi Arteta ko Wana wuri (Position) yake ganin Ricardo Calafiori zai iya bugawa?
Wani sabon labarin shiga nan👇👇

Nomba 3? Ko Kuma haryanxu baka yanke wurin (Position) da zaibuga ba?

Arteta: Zai iya buga kowana wuri, musamman idan yanayin salon wasan da mukeso mu buga da Kuma irin aikin da mukeso yayi mana. A salon wasanmu na yanzu dan wasane da zai dace damu sosai.

An tambayi Arteta akan farashin Smith Rowe yayi? Sannan farashin Calafiori yayi?

Arteta: Yace nayi matukar farin ciki da muka kammala siyo Calafiori. Kamar yadda nafada Ina tunanin samo wani dan wasan baya zai taimka mana sabida matsalar raunin Jurrien Timber. Hakan zai kara mana karfi a baya, domin zamu samo gasa a tsakanin yan bayanmu. Kuma zaisa Yan wasan namu su kara hazaka.

Meyasa kafi damuwa da gyara Yan wasan bayanka?
Arteta: Eh nayi hakanne sabida irin yadda muka Kare kakar wasa da ta gabata da yan wasa shida kadai. A irin haka ba karamin sa'a mukayi ba, wurin kare kakar wasan a hakan.

Willaim Saliba da Gabriel sun buga sama da kaso 50% cikin mintunan wasanni da muka buga a kakar wasa da ta gabata.

Bamu da tabbas ko zasu sake iya buga wannan wasanni nan da kakar wasa uku ko hudu a gaba. Wannan shine dalilin da yasa dole musake neman yan wasan baya.

✍️✍️✍️
Prince Tije

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post