LABARAN ARSENAL!! DALILIN DA YASA ARSENAL BASU SAYI AOUAR BA!!

Arsenal sun amince da kudin da kungiyar Lyon tasaka akan Housem Aouar!!

Kungiyar kwallo kafa ta Arsenal sun amince zasu biya kudin da Lyon tasaka akan Housem Aouar amma kudin da dan'uwan Aouar din wadda shine wakilin (Agent) din dan wasan yanemi Arsenal dasu bashi shine yahana Arsenal dasu dauko dan wasan.

Brahim Aouar wadda shine wakilin (Agent)din Housem Aouar ya nemi Arsenal dasu bashi kaso maiyawa wadda yakai 30% na abinda zasu biya akan dan wasan. Sai dai kungiyar ta Arsenal taki amincewa da tabashi wadannan kudin. Inda hakan yazama silar rashin dauko dan wasan.


Akwai yiwuwar kungiyar ta Arsenal sukoma kan dan wasan a watan january dan gudun karsu rasa dan wasan. Domin idan sukace zasu bar'dan wasan sai  zuwa karshen wannan kakar wasan (june/20201) to abune mai wahalar gaske su iya dauko dan wasan,  kasancewar manyan kungiyoyi irinsu.... Real madrid,  Juventus,  Psg duk zasuyo kan dan wasan.

Housem Aouar dai shine dan wasan da Arsenal keso ya maye mata gurbin Mesut Ozil. Domin yanzu haka shine kadai abinda kungiyar Arsenal tafi bukata. Lamba goma wadda ya'iya passing da rike kwallo.

Domin wannan position ne da Arsenal bata wasa dashi tarihin kungiyar.

Idan kunduba kungiyar Arsenal sundade batare da sunrasa Lamba 10 acikin kungiyarsu ba.

Tundaga kan irinsu..... Denis Bergkamp,  Cecs Fabregas,  Thomas Rocisky,  Samir Nasri,  Santi Cazorla,  Aaron Ramsey,  jack Wilshere,  har zuwa kan Ozil. Ancire Ozil acikin Team. Yanzu Arsenal basu da lamba 10. Hakan yasa suke duba yiwuwar komawa kan Housem Aouar a January. 
Duk da dan wasan yace zai kara zama a kungiyar na shekara daya hakan bazai hana idan aka bawa Lyon kudin dan wasan suki karba ba. Dan Aouar kamar kaddara yake ga kungiyar Lyon. Aduk lokacin da akabasu kudinsa to zasu sallamashi.

A wani labari da muke samu kuwa yana nuna Arsenal na duba yiwuwar neman matashin dan wasan tsakiyar kungiyar Red Bull Salzburg wato Dominick Szoboszlai.

Matashin dan wasan mai shekaru 19 dan kasar Hungry  salon wasansa kusan irin daya ne da na Housem Aouar. Wadda hakan yasa Arsenal suka fara sa ido akan dan wasan. Idan har Arsenal basu sami damar daukar Housem Aouar ba to zasu iya zuwa kan Dominick.



Wata kungiyar kwallo kafa dake kasar Saudi Arabia sunnuna sha'awarsu akan Ozil!?

Kungiar kwallo kafa ta Al-Nassr dake kasar saudi Arabia sunkaiwa Arsenal tayin €5m akan dan wasan tsakiyarsu wato mesult Ozil. Tare da yiwa dan wasan tayin kwantaragi shekaru 2 akan wasu manya kudade da ba'afadi yawansu ba.  Sai dai dan wasan ya shaidawa kungiyar ta Al-Nassr cewa shi bazai bar Arsenal ba har sai kwantaraginsa yakare da kungiyar ta Arsenal.


Mesut Ozil yana da kwantaragi shekara 1 da Arsenal wadda zai kare a karshen wannan kakar wasan. Dan wasan dai suna takun saka da kungiyar ta Arsenal inda rabon da yayi wasa a Arsenal tun a watan 3 na wannan shekara (7/3/2020) a wasan da Arsenal ta doke kungiyar Westham United a gasar Primier league.

Kushiha nan👇👇


Babu sunan dan wasan cikin jerin sunayen da kungiyar Arsenal ta mikawa Europa League na wadda zasu bugawa kungiyar wasanni rukuni (Group Stage) a gasar Europa leaue. Haka zalika abune mai wuyar gaske Arsenal su saka sunan dan wasan acikin wadda zasu bugawa kungiyar wasan Primier league zangon farko (First leg) za'amika sunayen yan wasa da zasu wakilci kowata kungiya a gasar primier league ranar 20/10/2020.


A daya bangaren kuma Mesut Ozil yabi sahun matasan Nigeria wurin nuna kin amincewa da ayyukan rundunan Sars.

Matasan Nigeria  musamman mazauna yankin kudu ne sukayi ta zanga zanga a zauren sada zumunta na Twitter akan rashin amincewa da ayyukan Sars tare da neman akawo karshen rundunar Sars akasar Nigeria.

Hakan yabiyo bayan wata yar tarzoma ce da tafaru tsakanin rundunar Sars din da matasan garin Lagos.

Matasan Nigeria dai sunyi takira ga gwamantin kasar Nigeria data rushe rundunar Sars sakamakon cin zarafin al'ummar kasar da Sars keyi.


Wadda hakan yajawo hankalin mutane a fadin duniya hartakai ga shima dan wasan tsakiyar Arsenal dan kasar Germany wato mesut Ozil yataya matasan nigeria din yaki da kawo karshen Sars.

Kushiga nan👇👇


Mum'munar labari akan abinda ke faruwa a kasar Nigeria. Mu watsa wannan labari zuwa ko'ina Yanar gizo dan kawo karshen Rundunar Sars. Ina jajantawa dukkan wadda al'amari ya shafa. Wannan shine abinda dan wasan yasaka a shafinsa na twitter.


Arsenal na kokari ganin ta tura willian Saliba aro (Loan) zuwa wata kungiya a England.

Dan wasan wadda Arsenal ta siyo daga kungiyar Saint Etienne na kasar a france a shekarar data gabata (2019) akan kudi €30m. Zai iya barin kungiyar zuwa wata kugiya a kasar England kafin arufe kasuwar yan kwallo na cikin gida (England) Arsenal dai nason tura dan wasan zaman aro (Loan) a wata kungiyar ne sabida dan wasan yasami damar buga wasa.

Matashin dan wasan mai shekaru 19 a duniya yana da bukatar lokacine da zai gane yadda yanayin kwallon kasar Ingila (England) yake inji Arteta. Hakan yasa mukeso muturashi zuwa wata kungiya inda zaisami isas'shen wasa zaifi ya zauna damu batare da yana taka leda ba.

Dan wasan dai yayi fama da jinya a kakar wasa data gabata,  wadda wasanni 15 kadai yabuga da kungiyar Saint Etienne. 
Dole dan wasan yana bukatar lokaci kafin yadawo taka leda yadda yakamata. 

Zamu taimakawa dan wasan matuka ganin wurin yazama babban dan wasa a duniya. Inji Arteta.

Kushiga nan 👇👇

Ana Alakanta dan wasan da komawa kungiyar kwallo kafa ta Brenford dake yammacin Birnin London dan ba'aso dan wasan yabar birnin London. Sai dai Arteta yace bazasu matsa wurin ganin dole sai suntura dan wasan aro (Loan) zuwa wata kungiya ba. Haryanzu dai kungiyoyi kasar England zasu iya cinikayya a tsakaninsu kamar daga Championship (Yan Relegation) zuwa Primier league. Ko daga primier league zuwa Championship (Yan Relegation) amma banda Primier to Primier.

Za'arufe wannan kasuwar ne ranar jumma'a mai zuwa. (16/10/2020).



Arsen Wenger ya yabawa kungiyar Arsenal inda yace zasu bada mamaki a wannan kakar wasan.

Kushiga Nan👇👇

Tsohon kocin na Arsenal wadda ya kwashe shekaru 22 yana aiki a kungiyar ta Arsenal. yace Arsenal zasu bada mamaki a wannan kakar wasan. Domin sunyi siyayya masu kyau, sun gyara masu tsaron bayansu.
Sunkuma tsawaita zaman wadda ya kamata su tsawaita.

Wenger ya shawarci Arteta da yaci gaba da taimakawa kungiyar kamar yadda yakeyi ayanzu. Ayanzu tawagar yan wasan suna da zuciyar tunkarar kowa,  inada tabbacin zasu iya samu maki (Points) fiye da yadda suka samu a kakar wasan da ta gabata. Kuma tabbas zasu sami Top 4th.


Lucas Torreira ya turawa Arsenal sakon fatan Alkhairi.

Kushiga nan👇👇

 Ina godiya ga dukkan mutanen da na samesu a Arsenal a wannan kyawawan shekaru biyu da nayi a kungiyar. Ka'ma daga hukumomi (Staffs) da nayi aiki dasu acikin fili da wajjen fili. Sannan zanso ace na rungumi dukkan magoya bayan Arsenal sakamakon soyayyar da suka nunamin tundaga ranar da nazo kungiyar.  Da wakar da suke reramin bazantaba mantawa dashi ba yana cikin raina. Ba karamin dama bace agareni na bugawa Arsenal wasa harna tsawon kakar wasa biyu.

Ina godiya matuka.

Torreira ya aikawa Arsenal da wannan sakonne a shafinsa na Twitter.

Tsohon dan wasan Arsenal dan kasar England wato Paul Merson ya yabawa Arteta akan siyo Thomas Partey.

Paul merson yace yana yabawa Arteta kan yadda yan wasan Arsenal ke kai kawo acikin fili. Pertey zai taimaka masu matuka.

Merson yace baisan meyasa manchester United ko Manchester City basu siyo Thomas Partey ba. Domin duk yafi yan wasan tsakiyar  (Midfielders) dasuke dasu ayanzu.



Kuci gaba da kasancewa damu dan samun labaran Arsenal acikin harshen hausa.



Admin
Prince Tije



Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post