Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta Mika tayin kudi har £30m ga kungiyar Norwich dan ganin ta dauke dan wasan tsakiyar Kungiyar wadda ta dade tana nema wato Emiliano Buendia.
Dan wasan mai shekaru 24 ya haskaka a kakar wasa da ta gabata inda ya taimakawa kungiyar ta Norwich City wurin haurowa gasar Primier League.
Darektan Arsenal wato Richard Garlick na kokarin ganin Buendia yazama dan wasa na farko da Arsenal zata fara siyowa a wannan kasuwar yan wasan.
Sai dai Norwich City din sunyi watsi da tayin na Arsenal.
Arsenal na fuskantar kalubale daga wurin Aston Villa Inda suma suka mika tayin £30m akan dan wasan.
Tsohon mai tsaron ragar arsenal watau emi martinez yabawa abokin wasansa na tawagar argentina emiliano buendia shawarar cewa yakyale Aston Vila yaje arsenal
Emi Martinez wanda yanzu haka yake taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Astonvilla bayan kammala komawarsa kungiyar daga arsenal a shekarar 2020 yafadawa abokin nasa cewa arsenal itace tafi dacewa dashi amatsayinsa na mai tasowa
Arsenal dai tamika tayin £30 million ga kungiyar Norwich city wadda ta hauro daga gasar gajiyayyu ta kasar ingila da maraicen ranar Alhamis saidai rahotanni sunce Norwich city tayi fatali da wannan tayin amma dukda haka tattaunawa nacigaba da wakana tsakanin kungiyoyin biyu
Saidai a wani bangaren kuma rahotanni sunce kungiyar kwallon kafa ta astonvilla suma sunkai tayin kudin na £30 million ga kungiyar ta Norwich city domin sayen dan wasan mai shekaru 24 wanda hakan zaisa sai inda danwasan yazaba
Emi buendia yataimakawa kungiyar Norwich wadda ta lashe gasar gajiyayyu takuma hauro zuwa gasar premier na kasar ingila inda yazama wanda yafi kowa taimakawa aci kwallo
Ana saran kafin a fara gasar copa america arsenal zata kammala daukar dan wasan wanda tadade tana tuntuba tun a watan janairun daya gabata
Kucigaba da bibiyarmu a shafinmu na arsenal zallah Facebook WhatsApp da kuma twitter kokuma a website namu www.arsnlzallah.com.ng
Admin
Ibrahim musa funtua