ARTETA YANA NEMAN JEFA ARSENAL ACIKIN WANI HALI!!

Mikel Arteta yazama daya daga cikin kochawa marasa basira a tarihin kwallon kafa ta duniya!!

Zakuyi mamakin jin wannan maganar tawa domin wannan shine karo na farko dana tabbatar da Arteta baida basira ko kadan a harkan kwallon kafa.

Dalilin da yasa nayi wannan maganar shine...

Arteta yana zuwa Arsenal Yayi fada da Ozil duk da nasan fadar Ozil bawai da Arteta ne kadai ba harda masu kungiyar kansu. To amma duk da haka shima Arteta yana da nasa laifin aciki 
Arteta yayi fada da Guendouzi wadda kowa yasani Guendouzi future player ne. Amma haka Arteta yacire Guendouzi acikin kungiyar Arsenal karfi da yaji.

Sabida son zuciya irin na Arteta yasaka karan tsana kawai akan Willian Saliba batare da yabashi dama ba. Yaro mai kyau amma haka Arteta yahanashi dama a Arsenal.

Yanzu kuma Arteta ya dauko hanyar fada da Aubameryang da Lacazatte.

Wannan wana irin rashin basira ce? Ace kana Coach Amma yan wasanka sune abokan fadanka? 

Arteta ya dauko hanyar kashe Arsenal.

Insha Allahu Arteta bazai wuce January a Arsenal ba.

Admin
Prince Tije

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post