Arteta yagama rikicewa yakasa gane meyakeyi ayanzu haka yana cikin rudani domin kuwa duk wata dabarar Arteta takare.
Abubuwan da suka dauremin kai nakasa fahimtarsu sune kamar haka...
Bayan zanga zangar da magoya bayan Arsenal sukayi a kwanaki baya na nuna rashin amincewarsu akan yadda Stan Kronke ke tafiyar da kungiyar Arsenal wadda wannan zanga zangar tayi sanadiyar mai kungiyar yasha Alwashin kawo gyara a ƙungiyar mussamn wurin siyo sabbin yan wasa.
Bayan haka shi kansa Arteta yayi magana akan cewa tabbas zasuyi gyara a wannan kakar wasan wadda hakan yasa magoya bayan kungiyar Arsenal sukaji karfi nacewa to tabbas Arsenal zasuyi gyara.
Amma abin mamaki sai gashi ba'akawo sabbin yan wasa da zasu kawo ci gaba a ƙungiyar ba, sai dai ma kara ragewa kungiyar karfi da akeyi.
Misali: haryanzu babu wani nomba 10 da aka kawo amma an rabu da Joe Willock wadda kusan zamu iya cewa yafara gogewa ba'a kawo wani ba amma anrabu da Willock.
Sannan ayanzu haka Arteta yana fada da Lacazatte da Aubameryang.
Duk da sun boye abinda ke faruwa akan al'amari abinda ke faruwa tsakanin Arteta da yan wasan biyu suka ce ae basu da lafiya ne.
Tun ranar jumma'a da aka sanar da maganar rashin lafiyar nasu naji ajikina cewa ba gaskiya bane. Nasan Awurin Ubangiji ba komai bane ya É—orawa yan wasan rashin lafiya a lokaci daya amma abin mamaki ne ace su biyun sun kwanta rashin lafiya a rana daya.
Sannan sai gashi tun jiya Asabar sai akecewa ma da wuya su buga wasan Arsenal da Chelsea.
Kenan yadda suka kwanta rashin lafiya rana daya haka zasu warke rana daya?
Kai daji kasan akwai raunin hankali aciki.
Tambaya ta anan shine su Balogun za'a sakawa a wasan Chelsea?
Duk lalacewar goma tafi biyar babu yadda za'ace wai Lacazatte ya lalace amma da Balogun za'ayi amfani.
Ayanzu haka Arteta baisan wa yake nema ba.
Duk wasu yan wasa da Arsenal Ke nema a yanzu sun hakura da maganar zuwa Arsenal sabida yanayin yadda Arteta yake nemansu.
Maddison yanason zuwa Arsenal Amma sabida son zuciya da rashin basira da rashin yadda ake Coaching Arteta yazabi Odegard akan Maddison wadda wannan tsantsar haukace.
Arsenal suka fara neman Lautaro Martinez Amma sabida hauka da rashin basira irin na Arteta sai Chelsea sukayi wuf sunje sun dauke Lukaku wadda hakan yasa Inter Milan bazasu bar Lautaro yabar kungiyar a yanzu ba.
Tammy Abrahm wadda yaso zuwa Arsenal kamar me yaki kula As Roma sabida Yana jiran Arsenal Amma daga karshe da ya fahimci cewa Arteta sha sha ne yau zaiyi Medical a As Roma.
Babu maganar Aouar babu kowa sai Odegard.
Yana fada da Lacazatte da Aubameryang.
Dan Allah wannan mutumin zamu kirashi amatsayin coach? Ko Ace mutumin da yasan kwallo??
Ina kudin da yataya Locatelli?
Ina kudin da aka saida Willock?
Wakuma Arteta yake nema?
Odegard din ma Loan zai amsoshi..
Ina takaici ganin Arteta a matsayin Kocin kungiyar Arsenal wlh.
Allah ya kawo karshe Arteta a Arsenal. Duk mai son Arsenal yace ameen.
Admin
Prince Tije