KOCIN BACERLONA YA BAYYANA DAN WASAN DA ZAI MAYE GURBIN MESSI

Kocin kwallon kafa na Bacerlona wato Ronald Koeman ya bayyana dan wasan da yake ganin shine zai maye gurbin messi a ƙungiyar.
Ronald Koeman ya bayyana Antonio Greizman a matsayin dan wasan da yake da kwari guiwa akan shi zai maye gurbin messi wadda ya koma kungiyar Psg dake kasar France.
Messi dai yabar kungiyar Bacerlona ne bayan da yashafe shekaru 21 a ƙungiyar yana taka leda. Acikin wadannan shekaru da messi ya kwashe a ƙungiyar yakasance dan wasa mai muhimmanci ga tawagar kungiyar kwallon kafa ta Bacerlona.

A kakar wasan da ta gabata messi ya sha wa Bacerlona kwallaye 30 a gasar La liga. 

Ronald Koeman yana fatan Anotnio Greizman ya gaji Lionel Messi a wannan kakar wasan.

Kocin yace yana da kwarin gwiwa akan Antonio Greizman zai haskaka a wannan kakar wasan bayan da Lionel Messi yabar kungiyar.

Shima Antoine Greizman ya karyata jita jitar da ake na cewa zai bar kungiyar Bacerlona a wannan kakar wasan.

Shin hakan yana nufin dama messi shine ya hana Greizman haskakawa a ƙungiyar kenan?

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post