ARTETA YAYI MAGANA MAI RATSA ZUCIYA BAYAN TASHI WADAN ARSENAL DA BRENDFORD


ARTETA YA FADI WASU MUHIMMAN ABUBUWA BAYAN TASHI WASA 


Hakikanin gaskiya nayi matukar bakin ciki abisa abinda yafaru  ,akwai hanyoyi da dama damuka so mufara kakar wasannan saidai hakan bai yiwuba ,wasan bai mana dadi ba kafin a tafi hutun rabin lokaci ,an jefa mana kwallo a raga amma daga baya yakamata ace munyi wani abu saidai bamuyi ba -cewar mikel arteta

Mikel arteta akan yan wasan gaba da basunan:

"Bazan karbi wani uzuri ba  ,magana ta gaskiya kenan mun rasa wasu yan wasan to amma ai munada wasu saboda haka babu boye boye ban bukatar wani uzuri"

Mikel arteta ya kara da cewa  "bamu cancanci mu dokesu ba ,inkanaso kayi abu na musamman  to yakamata ka kirkiri wani abu na musamman amma bamuyi ba  

Arteta akan fara kakar wasanni da rshin nasara :



"Wannan tarihi ne mai tsawo mun fara da daukar bakin ciki ,to zamu je mu kalli video yadda wasan ya wakana sannan muyi magana da kowa da kowa mugyara inda mukayi ba daidai ba kafin wasan sati muga ya za'ayi

Arteta akan cin da akayi ma Arsenal da throwing

"Abune mai matukar wahala sun tura mutum daya yaje ya rike golan mu ta baya da hannu yayi yunkurin ya motsa amma ina,kwallon ta shiga ciki amma su a tsarin premier sunce haka cine 

Arteta akan ko zai canza tsarin transfer 

"A a mu munsan wadanda muke bukata bana tunanin sakamakon yau zai canza mana tunani .

Sakon mikel arteta ga fans :

"Da fari dai ina gode musu saboda soyayyar da suke gwada mana musamman magoya bayan da suke binmu duk inda zamu  sannan daga karshe ina mai basu hakuri abisa wannan sakamako muna tabbatar musu da zamu farfado

Mai rahoto ibrahim musa funtua

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post