BACERLONA NA SHIRIN YIWA ARSENAL TAYIN DAN WASAN TSAKIYA AKAN AUBAMERYANG

Kungiyar kwallon kafa ta Bacerlona suna shirin kawowa Arsenal tayin musanye Coutinho da Aubameryang.

Bacerlona dae na fatan ganin sun raba Arsenal da kyaftin din nasu wato Aubameryang inda suke shirin yi masu tayin Coutinho da wasu kudi akan dan wasan gaban Arsenal din Dan kasar Gabon.

Sai dae Bacerlona suna neman Lacazatte shima inda suke fatan daukar yan wasan biyu Dukansu kafin arufe kasuwan musanye yan wasa na wannan kakar wasan.

Sai duk dan wasan da Bacerlona zasu dauka acikin Aubameryang da Lacazatte to zasu nemi musanye ne da wani dan wasan nasu domin ayanzu haka Bacerlona basu da kudin da zasu iya siyan wasu yan wasan.
A halin da ake ciki ayanzu haka akwai yar takun saka tsakanin Mikel Arteta da Yan wasan nasa guda biyu wato Aubameryang da Lacazatte.
Zuwa yanzu dai Bacerlona basu riga sun mikawa Arsenal tayin nasu na neman musanya Countinho da Aubameryang.

Amma rahotanni dake fitowa yanzu yanuna cewa Bacerlona sun shirya tsaf dan tunkarar Arsenal da wannan kasuwancin.

Kuci gaba da kasancewa damu dan jin wainar da za'a toya.


Shin zakuso wannan Deal din ta yiwu kuwa??

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post