BELLARIN YA BAYYANAWA ARTETA DA EDU BURINSA

Dan wasan bayan Arsenal Dan kasar Spain wato Hecotor Bellarin yana kokarin neman mafita wurin ganin yabar kungiyar Arsenal a wannan kakar wasan.

Bellarin mai shekaru 26 da haihuwa a duniya yana son barin kungiyar Arsenal a wannan kakar wasan inda kungiyoyi irin su Inter Milan da Ath Madrid duk suna zawarcin dan wasan.

Bellarin wadda a yanzu haka shine dan wasa da yafi kowa dade a ƙungiyar Arsenal yace a shirye yake da yarage Albashinsa inhar hakan zai sanya yabar kungiyar Arsenal.
Bellarin yana cikin yan wasa da kungiyar Arsenal Ke fatan rabuwa dasu a wannan kakar wasan sai dai haryanxu babu wata kungiya da takawowa Arsenal tayin kudi a kan dan wasan bayan nata dan kasar Spain.

A yanzu haka dai wasu rahotonni nacewa Arsenal tana iya yin musanye Bellarin da dan wasan bayan kungiyar Ath Madrid dan kasar England wato Kieran Tripper. Ko kuma dan wasan bayan Bacerlona wato Royal Emmerson.

Bellarin dai ya shaidawa Arteta da Edu burinsa na rage Albashinsa Dan yabar kungiyar Arsenal.

Shin zakuso Bellarin yabar Arsenal? 

Wana Dan wasa zakuso a kawo a matsayin wadda zai maye gurbin sa?

Kuci gaba da kasancewa damu dan samun labaran Arsenal acikin harshen Hausa

1 Comments

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment
Previous Post Next Post