MAKOMAR LACAZATTE A ARSENAL!!

Lacazatte zai iya barin kungiyar Arsenal kafin a rufe kasuwar musanye yan wasa na wannan kakar wasan.

Lacazatte wadda ayanzu haka suna takun saka da Mikel Arteta zai iya komawa kungiyar Bacerlona ko dae wata kungiyar daban.

Rahotonni da suke zuwa ayanu haka suna nuna cewa Arsenal na duba duk mai yiwuwa dan rabuwa da dan wasan mai shekaru 31 dan kasar France.

Ayanzu haka kungiyar Bacerlona itace kan gaba wurin neman Alexander Lacazatte.

Sai dai zuwa yanzu haka Bacerlona bata riga ta gabatar ga kudurinta ga Arsenal ba. Amma alamu sun nuna cewa Lacazatte zai iya barin Arsenal kafin nan da arufe kasuwar musanye yan wasa.
Sai dai babu tabbas ko Aubameryang zai bar Arsenal duk da wasu rahotonni nacewa Arsenal na son rabuwa da dan wasan bayan da suka sami damuwa da Arteta.

A jiya wasu rahotonni sunnuna cewa Bacerlona na bukatar Aubameryang da Lacazatte ne amma dole sai sun saida Braithwaite kafin zasu iya kawo wa Arsenal tayin siyan yan wasan nasu.

Amma zuwa yanzu rahotonni na nuna cewa Arsenal zasu iya saida Lacazatte ga duk wata kungiyar da takawo tayi neman dan wasan. Inda zasu cigaba da rike Aubameryang.

Wa zakuso a saka tsakanin Aubameryang da Lacazatte?

Admin
Prince Tije

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post