MAGOYA BAYAN ARSENAL SUN KASU GIDA BIYU BAYAN EDU DA ARTETA SUN CIMMA WATA MATSAYA


MAGOYA BAYAN ARSENAL SUN KASU GIDA BIYU BAYAN EDU DA ARTETA SUN CIMMA WATA MATSAYA

Magoya bayan kungiyar arsenal sun banbanta a Ra'ayi bayanda sukaji cewa granit xhaka ya saka hannu a sabon kwantiragi na tsawon shekaru hudu da arsenal



Xhaka wanda a kwanakin baya dasuka wuce aka dinga alakantashi da komawa kungiyar As Roma ya tsawaita kwantiragin ne har zuwa shekarar 2025

Saidai kara kwantiragin baizoma wasu magoya bayan kungiyar da dadiba yayinda wasu kuma murna har baka



Xhaka yasamu damuwa tsakaninshi da wasu magoya bayan arsenal wanda hakan yasa dangantaka tayi tsami tsakaninshi da magoya bayan arsenal din sosai

Shin yaya kuke kallon wannan kara kwantiragin na xhaka yayi daidai kokuwa ?

Mai rahoto ibrahim musa funtua

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post