Kalaman Arteta bayan antashi daga wasan Liverpool.
Arteta: naji takaici sosai. Mun yi duk abin da za mu iya don sanya manyan yan wasan da suka dace wadda zasu iya tunkarar Liverpool. Mun fara wasan da kyau, amma munyi saken sun sakan mana kwallon da wuri.
Arteta akan jan katin (Red Card) Thomas Partey
Babban hasara ne faruwa hakan. Dole ne mu koyi yadda zamu dinga kiyaye hakan. Mun buga wasanni uku kenan inda muke kare wasan da yan wasa goma acikin filin wasa kuma a kan manyan kungiyoyi. Ba abin da muke bukata ba kenan daga yan wasan mu.
Arteta akan Tomiyasu:
"Ya yi abin ban mamaki. Ba mu so ya taka leda a wannan wasan ba amma a halin da muke ciki na rashin Cedric da Chambers, yasa yace yana son buga wasan, domin ko atisaye baiyi ba.
Wadannan sune kalaman Arteta bayan Antashi daga wasan da Liverpool ta doke Arsenal daci 2-0 a jiya.