Gunners - wadanda suka ba da aron Folarin Balogun da Ainsley Maitland-Niles a makon da ya gabata - suna da 'yan wasa uku da Suka halarci gasar cin kofin Afirka da kuma Yan Wasan masu rauni da yawa, amma dan wasa daya ne Martin Odegaard, shine yake da Covid.
Tottenham ta yi imanin cewa ba a tsara dokar da ta Shafi a jinkirta Wasa ba don irin waɗannan yanayi kuma sun nemi Premier League don Ayi ƙarin haske, musamman ganin yadda aka ƙi karbar nasu buƙatun a baya.
Sanarwar ta ce: ‘Muna Nadamar sanar da cewa an dage karawar da za a yi da Arsenal a arewacin London ranar Lahadi.
'Wannan ya biyo bayan matsaloli da Arsenal take fuskanta a gasar Premier bisa ga hada-hadar Covid, wadanda suka samu raunuka da na baya-bayan nan da kuma 'yan wasan da ke taka leda a gasar cin kofin Afrika.
"Mun yi matukar mamakin cewa an amince da wannan Bukatar inji Tottenham"
"Mu da kanmu an kore mu daga Gasar Cin Kofin Turai bayan yawancin Yan Wasan mu da suke da Covid da ke nufin muna buƙatar sake tsara jadawalin Wasanni