Arsenal na neman tsohon dan wasan Chelsea, Diego Costa
Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta gudanar da bincike Akan tsohon dan wasan k Chelsea, Diego Costa.
Dan wasan mai shekaru 33 ya kusa kammala yarjejeniya da kulob din Atletico Mineiro na Brazil kan batun kawo karshen kwantiraginsa kuma Goal ta ruwaito cewa Gunners ta tuntubi dan Wasan dan.ganin ko dan wasan zai so komawa gasar Premier.
Costa ya yi alfahari da bajintar da ya taka a kan Gunners a lokacin da yake tare da Chelsea, sannan kuma ya ci wa Atletico Madrid kwallaye masu mahimmanci a wasan dab da na kusa da karshe na 2018 na Europa, wanda ya kawo karshen fatan Arsene Wenger na kammala kakarsa ta karshe a Emirates da kofi.
Sai dai kuma an ce tsohon Dan Wasan na gaba baya gaggawar yanke shawara akan makomarsa kuma a halin yanzu yana hutu a Spain. Har yanzu Arsenal ba ta kai tayin ba, yayin da Costa yake Kara yin Farin jini agurin kungiyoyi kasarsa ta Brazil ciki har da Corinthians.
Mikel Arteta yana matukar Sha'awar karfafa Yan Wasan a cikin abin da ya rage a kasuwar musayar 'yan wasa ta Janairu tare da bayyana makomar Pierre-Emerick Aubameyang yayin da yake bakin aiki a gasar cin kofin Afrika.