Emile Smith Rowe, Takehiro Tomiyasu da Kieran Tierney duk sun halarci atisayen na Arsenal a ranar Talata.
Tawagar Mikel Arteta sun kammala rangadin da suke yi na tunkarar kakar wasa ta bana a Amurka kuma yanzu sun koma Landan domin ci gaba da shirye-shiryensu na tunkarar sabon kamfen.
Yanzu haka Arsenal za ta buga wasan sada zumunta da Brentford a filin wasa na London Colney ranar Laraba kafin su kara da Sevilla a filin wasa na Emirates ranar Asabar.
Gabanin wasan da Brentford, Arteta ya samu kwarin gwiwa yayin da Tierney, Smith Rowe da Tomiyasu suka yi atisaye a London Colney ranar Talata.
Tierney da Smith Rowe sun kasa taka rawar gani a rangadin da Arsenal ta yi a Amurka saboda rauni, yayin da Tomiyasu bai taka leda ba a wannan bazarar.
Sai dai har yanzu sabon dan wasan da suka dauko fam miliyan 34 Fabio Vieira bai samu dama yin wasa, yayin da yake ci gaba da murmurewa daga raunin da ya samu a kafarsa.
Wataƙila Fabio ya ɗan daɗe, ”in ji Arteta
'Ina ganin yana bukatar wani mako ko makamancin haka kafin ya fara aiki da kungiyar amma yana aiki tukuru kuma ya yi rashin sa'a da ya fara taka leda a Arsenal ta wannan hanya amma kuma ya dace sosai.'
A ranar 5 ga watan Agusta ne Arsenal za ta fafata da Crystal Palace a gasar Premier.