Martin Ødegaard: zuwa yanzu sabbin yan wasanmu suna matukar kokari sosai. Suna aiki tuƙuru kuma dukkansu suna da dabi'u masu kyau. Zasu kawo wani abu mai kyau ga ƙungiyar.
Fabio yana da rauni amma munga yadda Matt Turner da Gabriel Jesus suka taka rawar ganin sosai a wasannin da muka buga. Don haka ina ganin duk zasa taimaka mana.
Musamman Gabriel Jesus zanji dadin yin Wasa kusa da Gabby a gaba, Ina tsammanin zai kasance abu mai da daɗi a gareni sosai.
Ina tunanin sabbin yan wasan da suka zo kungiyar zasu inganta wasu abubuwa a cikin kungiyar, kuma ina tsammanin duk 'yan wasan da aka siyo sun kawo wani abu mai kyau wurin karawa yan wasan da suka kungiyar hazaka da kuma maida hankali akan abinda mukeso muyi.
Sun kawo kyakyawar karsashi acikin kungiyar Sun karawa tawagar yan wasan kwarin guiwa a ciki da wajen filin wasa mutanen kirki ne. Wannan yana da mahimmanci ga ƙungiyar.
“Dukkanmu mun ji takaici a karshen kakar wasa ta bana, bayan da muka rasa mataki na hudu. Munyi sakaci dashi bayan mun same shi a hannunmu, don haka abin takaici ne matuka, don haka ina ganin za ku ga kungiyar Arsenal dake da jin yunwar nasara a wannan a wannan kakar wasan.