SABON DAN WASAN ARSENAL ZINCHENKO YA BAYYANA WANI ABU DA YA GANI ARSENAL

Zinchenko: Abin farin ciki ne sosai zuwana Arsenal kuma na yi farin ciki da sakamakon da muka samu akan Chelsea. Munyi wasa mai kyau ba shakka. amma har yanzu akwai wasu abubuwa da za mu iya gyara.


 Doke kungiya irin Cheslea daci 4-0 babban sakamako ne, amma wannan wasan sada zumunci ne kawai,  a gasar Premier zai bambanta.  Ina fatan sakamakon zai kasance iri É—aya, amma muna buÆ™atar yin aiki tuÆ™uru.  Ina buÆ™atar sabawa  da wuri-wuri kuma na fara jin daÉ—in abokan wasana sosai kuma ina jin daÉ—insa kasancewa ta a Arsenal.

 Ina mika sakon  godiya mai ga abokan wasa na da, dukkan ma'aikatan dake bangaren horaswa da kuma ma'aikatan lafiya saboda kyakkyawar tarba da suka yimin  hakan ya taimaka min sosai. Akwai 'yan wasa masu kyau da yawa kuma na fahimci irin girman da suke dashi.

 Daya daga cikin manyan dalilan da yasa na zo Arsenal shine kocinmu Mikel Arteta.  Na san shi sosai tun lokacin da na ke Manchester City kuma kar ku manta cewa tun ina yaro Arsenal ce  kungiyar da nakeso, don haka burina ya zama gaskiya.

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post