RAHOTANNI DA SUKE FITOWA A YAU SUNA CEWA ARSENAL ZATA IYA RASA DAN WASAN TA

Rahotanni da suke fitowa a yau sun ce Pablo Mari na iya komawa kungiyar Kwallo kafa ta Fenerbahce a matsayin aro a kakar wasa mai zuwa.

Dan Wasan na Sipaniya  ya shafe rabin na biyu na kakar wasan data wuce  a Seria A tare da kungiyar Udinese, Amatsayin aro kuma yana É—aya daga cikin sunayen da aka fi dangantawa   da barin kungiyar Arsenal a wannan bazara.

Dan wasan mai shekaru 28, ya buga wasanni biyu kacal a gasar Premier a kakar wasan da ta wuce, inda ya buga wasan farko da Brentford da Chelsea.

Da aka ba shi lokaci mai tsanani inda Romelu Lukaku ya samu dama ya zurawa Arsenal Kwallo a filin wasa na Emirates, dan wasan ya sake buga wasa sau daya - a gasar cin kofin EFL da aka doke AFC Wimbledon da ci 3-0 - kafin ya tafi aro a watan Janairun da ya gabata.

A halin yanzu dai Jorge Jesus ne ke jagorantar kungiyar ta Turkiyya, tsohon kocin Flamengo wanda ya san Mari sosai bayan ya yi aiki a can. din

Akwai maganar biyan Arsenal kudin lamuni na Yuro miliyan 5, wanda ake ganin zai yi  matukar Wahala kuma ba zai yuwu su iya biya ba, amma kamar yadda Mikel Arteta ke da niyyar rage yan wasan kungiyar, a matsayin yunkuri  da zai iya kawo wata mafita Mai ma'ana ga duk wanda abin ya shafa.

Tun zuwansa daga Brazil a watan Janairun 2020, Mari ya buga wasanni 22 kacal a duk gasa da yayi Arsenal

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post