Abin da ya kamata ku sani ranar rufe kasuwar cinikin 'yan wasa a Premier
Transfer last day
Daren ranar Alhamis za a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan kwallon kafa a wasu kasashe a nahiyar Turai har da Ingila - Mohammed Abdu ya hada muku abubuwan da ya kamata ku sani kan cinikayyar da aka yi.
Kasuwar bana ta Premier League ta fara ci ranar 10 ga watan Yunin 2022, da zarar an kammala cinikayyqar ranar Alhamis 1 ga watan Satumbar 2022 - sai ranar 1 ga watan Janairun 2023 za a sake bude kasuwa.
Tuni kungiyoyin Premier League sun kashe kudi kusan £1.7bn a kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo da za a kammala hada-hada a tsakar daren Alhamis.
A kakar 2017 aka yi cefane mai tsada kan £1.43bn.
An samu karin cinikayya bayan cutar korona da ta kai tsaiko a kaka biyu baya musamman karancin rashin samun kudin shiga ga kungiyoyin - an kashe £1.1bn a bara.
Kungiyoyi bakwai a Premier sun dauki 'yan wasa a matakin mafi tsada a tarihin kafuwarsu kan kudi sama da £30m kowanne a kakar cinikayya ta 2021.
Za a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo a English Premier League da kuma Football League teams da karfe 23:00 GMT ranar Alhamis 1 ga watan Satumba, awa daya tsakani a rufe ta Scotland.
A kasar Sifaniya, inda Barcelona ta kashe dan karen kudi wajen sayen 'yan kwallo a bana, za a rufe kasuwar da karfe 23:00 a Faransa kuwa da karfe 22:00.
Za a rufe kasuwar Italiya da karfe 19:00 ta Jamus kuwa za ta watse da karfe 17:00 ranar Alhamis.
Cefanen da aka yi a gasar Premier League:
Manyan kungiyoyin Premier League sun dauki 'yan kwallo 143 - fiye da 128 da aka saya a 2019 da 132 da aka dauka a 2020.
A bara an sayi 'yan wasa 14 a ranar karshe da za a rufe kasuwa - mafi karanci da aka yi hada-hada a ranar karshe ta rufe kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo.
Tuni Manchester United ta kulla yarjejeniyar da Ajax, domin daukar dan kwallon Brazil, Antony, mai shekara 22.
Idan United ta kammala cinikin da ake cewar zai kai £81.3m - zai zama na hudu da aka saya da tsada a tarihin
Barcelona na gab da daukar Hector BellerÃn. Dan wasan yana jiran kiran karshe don shiga Barça sannan ya sanya hannu kan kwantiragin - baya karbar shawarwari daga Italiya don shiga FCB. 🚨🔵🔴 #Ranar Karshe
Pierre Emerick Aubameyang ya dawo Landan domin komawa Chelsea daga Barca kan yarjejeniyar shekaru biyu tare da zabi na uku.