Tsohon Mai tsaron bayan Italy Bonucci yayi magana akan Richard Calafiori.
Banji dadin tashinsa a Bolgona ba. Zanso ganinsa a Juventus. Mai tsaron bayane da yake da abubuwan da suka Sha banban da wadanda Muka saba gani awurin masu tsaron baya.
Dan wasan bayane da yake da basira. Zai zama abinda kwantace ga Yan wasan Italy masu tasowa nan da shekaru 15.
Mikel Merino Yace Yana da bukatar ya natsu domin zaban kungiyar da zai koma taka leda bayan da ya yanke shawarar bazai Kara Sanya hannu a Sabon kwantiragi da Real Sociedad ba.
A halin yanzu kungiyar da tafi matsawa akan siyan dan wasan itace Ath Madrid. Arsenal ta kira Real Sociedad akan dan wasan amma haryanxu basu mika tayinsu akan dan wasan ba.
Mai tsaron bayan Arsenal dan kasar Japan Tomiyasu yasami rauni a guiwarsa wadda hakan hakan yasa baya cikin tawagar yan wasan Arsenal da sukaje America buga wasanni share fage.
Jaridar CBS tace dan wasan bayan zaiyi jinya Harna tsawon makonni uku. Wadda hakan ke nufin dan wasan bazai buga wasanni share fage kwata kwata ba.