Mikel Arteta Akan Wasan Arsenal da Manchester United


Mikel Arteta akan nasarar da Arsenal tayi akan Manchester United daci 2-1.

Wannan gwaji ne Mai kyau a garemu.  Buga wasan a wani fili na daban , wadda yake da wani yanayi na daban,  filin wasa da yasha banban da irin filin wasa da muka saba buga wasa aciki, sannan muna fara wasan aka saka mana kwallo a raga.

Buga wasa a irin wannan yanayi abune mai a garemu, muga irin matakin da muke da Kuma abinda zamu iya yiwa wurin gyara wasanmu dan yin nasara a wasan, nayi matukar farin ciki da irin wannan yanayi.

Arteta akan sakon da ya isarwa yan wasan Arsenal bayan tashi daga wasan.

Nafada masu wannan wani gwaji ne, bawai samun maki ukun da mukayi a wasan bane kadae, akwai abubuwa da yawa agabanmu nasan kuma kunga haka. Ina tunanin kungiyoyin biyu sunyi kokari, Manchester United sun buga wasa na kwarewa sosai.

Wannan shine abinda kake bukata dan ka kara shiryawa wasanni a gasar Primier League da Kuma champion league.

Yana da kyau ka fahimci Ina kungiyarka ta dosa tun wuri.

Mikel Arteta akan magoya bayan Arsenal a filin wasa na Sofi Stadium. Muna godiya kwarai da xuwa kallonmu da sukayi. Muna fatan sunji dadin kallon wasanmu, sannan dafatan mun nishadantar dasu.

Wannan filin wasa ne mai ban sha'awa, filin wasa ne da ya banbanta da irin wadda muka saba wasa aciki.

Hasken wuta ne ta ko'ina, ga hayaniyar mutane, da wakoki da muryoyin mutane ta ko'inam abune da ya kasance na daban a garemu, amma duk da haka munji dadin taka leda a filin wasan. Muna godiya sosai

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post