*Salon wasansa*
Ricardo Calafiori bahago ne wadda yafara wasansa a matayin dan wasan baya mai buga lamba 3 gefen hagu. Haka zalika dan wasan yana buga gefen hadu idan za'ayi amfani da yan baya mutum uku.
Bayan Calafiori yakoma Bologna mai horas da kungiyar Bolgona Thiago Motta ya maida dan wasan lamba 5 sabida kwarewarsa da yake dashi wurin iya dogon passing da kuma iya shiga da kwallo gaba, wadda hakan yasa dan wasan yazama daya daga cikin mafi kyaun mai tsaron baya a gasar Seria A, a kakar wasan ta 2023/2024.
Calafiori yana iya buga nomba 5 idan Mai horaswa ya zabi yayi amfani da yan baya mutum hudu wato Back four. Domin kuwa dan wasan yana da zafin nama gashi da karfi da Kuma iya damun nomba 9.
Calafiori yana da zafin nama, sannan Yana da duma sosai musamman daga nesa. Tsayin Calafiori yana bashi dama wurin iya cire kwallo ta sama. Kwarewa wurin iya daukar kwallo daga baya ya shiga da'ita yana daga cikin abubuwan da yasa dan wasan bayan yakara zama daya daga cikin manyan yan Wasa a gasar Seria A.
Kishiga nan dan samun sabbin labarai👇👇
*CALAFIORI A NOMBA 3*
A duk sanda dan wasan yake buga nomba 3 yana iya daukar kwallo ya shiga gaba da'ita wato yana da attacking a nomba 3. Yana iya taimakawa aci kwallo sosai a nomba 3. Sannan yana iya tare wato defending, sannan yana iya dawowa da sauri yayi defending a duk lokacin da ya tafi gaba.
Ana yiwa Dan wasan kallon dan wasan baya mafi kyau a yanzu haka. A shekarar 2019 Calafiori ya shiga cikin sahun matasan yan wasan duniya guda 60 masu tasowa wadda Jaridar Guardian ta fitar.
Haka zalika Calafiori ya shiga cikin sahun matasan yan wasa 50 masu tasowa a nahiyar turai a shekarar 2021.
✍️✍️✍️
Prince Tije