Ricardo Calafiori matashin dan wasa dan kasar Italy mai shekaru 22 a duniya.
An haifi dan wasan a ranar 19/5/2002.
Dan wasan yafara taka leda a kungiyar As Roma tun yana karami. A shekarar 2018 dan wasan ya sanya hannu a Babban kwantiragi da As Roma. Sai dai a wannan shekarar dan wasan ya sami mum'munar rauni a guiwarsa wadda yayi sanadiyar ya dauki tsawon watanni batare da ya taka leda ba.
Ku dannan Nan👇👇
Calafiori yafara buga wasa na farko da As Roma, sannan farkon wasansa a gasar Seria A a wasan da As Roma ta doke Juventus daci 3-1. A ranar 2/10/2020 a wannan wasan Calafiori ya sami bugun daga kai sai Mai tsaron raga inda abokin wasansa na As Roma Perroti yayi bugun daga kai sai Mai tsaron ragar.
A ranar 3/12/2020 Calafiori ya shigo a chanji inda ya chanji Spanizolla a gasar Champion League a wasan da As Roma ta buga da Young Boya.
shigansa ke da wuya ya zura kwallo a raga. A ranar 14/1/ 2022 As Roma suka tura Calafiori zaman aro a kungiyar Genoa.
*Basel*
A ranar 30/8/2022 As Roma ta sanar da siyar da Calafiori zuwa kungiyar Basel. Inda dan wasan ya sanya hannu a kwantiragi shekaru uku da Basel. Calafiori ya fara atisaye da kungiyar Basel a karkashin Mai horaswa Alexender Frei. Inda yarara wasa na farko da Basel a ranar 22/10/2022 a wasan da Lugano ta doke Basel daci 1-0.
*BOLOGNA*
A shekarar 2022 Calafiori ya koma kungiyar Bolgona daga Basel a karkashin Mai horaswa Thiago Motta
✍️✍️✍️
Prince Tije